Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce a dare daya ya magance yajin aikin malaman jami’o’i ta kasa ASUU lokacin mulkin sa.
Jonathan ya bayyana hakan ne da ya ke zantawa da manema labarai ranar Laraba a birnin Abuja yayin bikin cika shekaru 70 na babban mai bishara Bishop Hassan Kuka na jihar Sokoto.
A lokacin mulkin shugaba Jonathan, kungiyar malamai ta ASUU ta yi yajin aiki da ya kai watanni hudu.
Tun farko shekarar 2022 yan kungiyar ta ASUU suka tsunduma yajin aiki, suna bukatar gwamnatin tarayya ta cika alkawuran da ta dauka musu na inganta harkar ilimi da tsarin biyan albashi, sai dai an kasa samun daidaito tsakanin gwamnatin da kungiyar malaman, lamarin da ya sa dalibai kwashe fiye da watanni shida a gida.
Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan na ganin cewa rashin shugaban ci na gari shine musabbabin ci gaba da yajin aikin kungiyar malaman.
Ya kuma shawarci yan Najeriya su kare martabara demokoradiyya a kasar.