A GUJI YA’DA JITA-JITA, INJI KWAMISHINAN ‘YAN SANDAN JIHAR IMO

A GUJI YA’DA JITA-JITA, INJI KWAMISHINAN ‘YAN SANDAN JIHAR IMO

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo CP Hussaini Rabi’u yayi kira ga’ yan asalin jihar da sauran al’ummomin dake zaune a jihar da su kiyaye mabarnatan mutane masu yada labaran karyar da ba su da tushe balle mafari.

Wannan na kunshe ne a cikin wata takardar manema labarai mai dauke da sa hannun Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar CSP Michael Abbattam wadda aka aiko ma WTV.

CP Rabiu yayi wannan kiran ne a lokacin da yake mayar da martani kan wasu jita-jitan da aka yada a ranar Litinin 4 ga watan Oktoba cewa wai wasu batagari sun kitsa tada zaune tsaye don kawo cikas ga zaman lafiyar da aka samu.

Kwamishinan yace irin wadannan labaran karya na iya ba barayi damar yin sace-sace da saka rayuwar al’umma cikin hatsari.

CP Rabiu yace amma duk da haka rundunar ‘yan sandan bata yi kasa a gwiwa ba wurin aika dakaranta a karkashin jagorancin Mataimakin Kwamishina mai kula da gudanar da aiki don zagayawa suga gaskiyar lamarin, inda suka ga cewa abun da ake yadawa ba gaskiya ba ne, kuma suka umurci shugabannin ofisoshin yanki na ‘yan sanda da su sa ido kan abubuwan dake gudana.

CP Rabiu ya bukaci al’ umma da su yi watsi da duk wani umurnin da wani zai bayar wanda ba na gwamnati ba. Kuma su sanar da hukuna mafi kusa ko su kira lambar kar ta kwana 08034773600.

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *