ADAMA BARROW YA LASHE ZABEN SHUGABAN KASAR GAMBIYA
Shugaban Kasar Gambia mai ci Adama Barrow ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar asabar da ta gabata.
Barrow wanda ya fafata a zaben a karkashin tutar jam’iyyar NPP, ya samu kuri’u 457, 519 inda ya doke abokin hamayyarsa Ousainou Darboe na jam’iyyar UDP wanda ya samu kuri’u 238,253, kamar yadda shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Alieu Momar Njai, ya tabbatar.