ALLURAN RIGAKAFIN KORONA MILIYAN 1 SUN LALACE A NAJERIYA KAMUN AYI AMFANI DA SU

ALLURAN RIGAKAFIN KORONA MILIYAN 1 SUN LALACE A NAJERIYA KAMUN AYI AMFANI DA SU
No photo description available.
An kiyasta cewa alluran rigakafin Korona miliyan daya ne suka lalace a Najeriya a watan da ta gabata ba tare da anyi amfani da su ba, kamar yadda majiyoyi biyu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Lamarin Wanda shine daya daga cikin mafi girman asarar allurai da aka samu, na nuna wahalar da kasashen Afirka ke fama da su wajen yin allurar ta rigakafin Korona.
Rahoton ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mafi yawan al’umma a Afirka, da suka kai miliyan 200, wanda kawo yanzu kashi 4% ne kadai aka yi wa cikakkiyar allurar riga-kafi, kamar yadda kididdigar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta nuna.
Wata majiya ta uku da ke da masaniyar isar alluran Najeriya tà tabbatar dà cewa wasu daga cikin alluran sun iso ne makonni hudu zuwa shida na lalacewarsu kuma ba za a iya amfani da su cikin lokacin da ya rage ba, duk da kokarin da hukumomin lafiya suka yi.
Wani mai magana da yawun Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta kasa, da ke da alhakin allurar rigakafi a Najeriya ya ce ana ci gaba da daukan kididdigar adadin allurar rigakafin da aka samu da kuma wandanda aka yi amfani da su, kuma za’a bayyana sakamakon binciken cikin kwanaki masu zuwa.

GUDUMMAWA:

Tabbatar da tsabtataccen aikin jarida, abu ne da ke da muhimmin amfani wajen wanzuwar zaman lafiya, ilimantar da al’umma kan lamuran yau da kullum, da kuma kauracewa duk wani abinda zai jawo rudani ko tashin hankali. A dalilin haka ne muke bukatar gudummawarku domin dorewar wannan kokarin. Domin bada gudammawa, ga bayanan asusun banki:

Jaiz Bank Account lamba:

0001741269

Wonderland Television ltd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *