AN AYYANA DOKAR TA ‘BACI A ‘KASAR SOMALIYA SABODA FARI’

AN AYYANA DOKAR TA ‘BACI A ‘KASAR SOMALIYA SABODA FARI’
Firaministan Somaliya Mohamed Hussein Roble ya ayyana dokar ta baci sakamakon matsalar fari da kasar ke fuskanta.
Sanarwar ta zo ne bayan da firaministan ya jagoranci wani taron majalisar zartarwa na musamman a ranar Talata da ta gabata, inda ya yi kira ga al’ummar Somaliya da kasashen duniya da su taimaka wa wadanda farin ya shafa.
Mummunan fari dai ya addabi yankuna da dama a kasar, lamarin da ya jefa kimanin mutane Milyan 3.5 da dabbobi cikin mawuyacin hali. A wasu yankunan kuma ta kashe wasu da kuma dabbobi.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce farin ya kara ta’azzara sakamakon gazawar ruwan sama a karo na uku tun daga karshen shekarar 2020

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *