AN CAFKE WANI ‘DAN SANDA DA YA HARBE WATA ‘YAR SHEKARA 8

AN CAFKE WANI ‘DAN SANDA DA YA HARBE WATA ‘YAR SHEKARA 8

An kama wani dan sanda da laifin kashe wata yarinya ‘yar shekara takwas a birnin Bamenda na kasar Kamaru ranar Juma’a, yayin da ya harbi wata mota da ta tsere daga wani shingen bincike, in ji gwamnatin ‘kasar.

Mutuwar yarinyar dai ta haifar da kazamin zanga-zanga da yammacin ranar Juma’a inda akalla mutane biyu suka samu raunuka, kamar yadda wata majiya mai tushe ta bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *