AN CAFKE WASU MATASA DA SU KA ADDABI JIHAR SOKOTO

AN CAFKE WASU MATASA DA SU KA ADDABI JIHAR SOKOTO

Rundunar Tsaro da Bada Kariya ga Farar Hula reshen jihar Sakkwato ta baja koli ga manema labarai na wani gungun mutanen da ake zargi da fashi da makami da satar dabbobi.

Wannan na kunshe ne a cikin wata takardar manema labarai mai dauke sa hannun Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, DSC Hamza Adamu wadda aka aiko ma WTV.

Takardar ta bayyana cewa rundunar a karkashin jagorancin Kwamanda Muhammad Saleh Dada ta kama wa’yanda ake zargin ne a Fadamar Lugu dake gundumar Giyawa ta karamar hukumar Wurno.

A cewar takardar, dakarun rundunar dake karamar hukumar Wurno tare da hadin gwiwa da kungiyar ‘yan sakai suka kama mutane 7 tare da gano dabbobi 54.

Barayin dabbobin da aka kama sune Buba Alhaji Bello (Dan delu) mai shekaru 20, da Abdullahi Hassan (yellow) mai shekaru 22, da Alti Shehu dan shekara 25, da kuma Sani Alhaji Duna mai shekaru 18.

Sauran mutanen daka aka gabatar kan laifin satar dabbobin sun hadda da Abu Gidado dan shekara 20, da Shehu Modibbo (Dan Acha) mai shekaru 20, da kuma Ibrahim Modi (Major) mai shekaru 20.

Haka kuma an
gabatar da wasu mutane biyu da ake zargi da aikata fashi da makami tare da masu ba su bayanan sirri da aka kama a Dabagi Lafiya ta karamar hukumar Dange Shuni

Mutanen sun tabbatar da cewa suna da hannu a wata ta’asar da aka aikata sau biyu a Lambar Tureta da Dorawa wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane 6 tare da sace wasu.

Mutanen biyu sun hada da Muhammad Aminu mai shekaru 20 da Buba Alhaji Garba dan shekara 30. Masu bada bayanan sirrin sune Umar Sanda mai shwkaru 48 da Nura Bello dan shekara 34.

GUDUMMAWA:

Tabbatar da tsabtataccen aikin jarida, abu ne da ke da muhimmin amfani wajen wanzuwar zaman lafiya, ilimantar da al’umma kan lamuran yau da kullum, da kuma kauracewa duk wani abinda zai jawo rudani ko tashin hankali. A dalilin haka ne muke bukatar gudummawarku domin dorewar wannan kokarin. Domin bada gudammawa, ga bayanan asusun banki:

Jaiz Bank Account lamba:

0001741269

Wonderland Television ltd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *