
AN CAFKE WATA MATA MAI SAFARAR MAKAMAI WA ‘YAN BINDIGA
Jami’an ‘yan sanda a jihar Zamfara sun yi nasarar cafke wata mai suna Fatima Lawali, ‘yar asalin karamar hukumar Kaura Namoda wacce ta kware wajen samar da makamai da alburusai ga ‘yan bindiga a jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Katsina da Neja.

An kama wanda ake zargin ne a unguwar Gada Biyu da ke karkashin karamar hukumar Bungudu dauke da harsasan bindiga kirar AK-47 guda dari tara da casa’in da daya (991) da ta ‘dauko daga Kauyen Dabagi da ke Jihar Sakkwato domin kai wa wani kasurgumin dan fashin nan mai suna Ado Alero da ya addabi jihar Zamfara, da jihohin da ke makwabtaka da su.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ayuba N. Elkanah ne ya bayyana hakan a cikin wata takarda da ya sanya hannu