AN FARA TARON BAJE KOLIN SHIRYE-SHIRYEN HOTUNAN BIDIYO TA CABSAT 2021 A BIRNIN DUBAI

AN FARA TARON BAJE KOLIN SHIRYE-SHIRYEN HOTUNAN BIDIYO TA CABSAT 2021 A BIRNIN DUBAI

Mashahurun kamfanoni masu watsa hotunan bidiyo ta hanyar tauraran d’an adam da dillanci Labaru da sauran watsa shirye shirye a gabas ta tsakiya, nahiyar Afrika da kuma kudancin Asiya na halartar taron Baje Kolin CABSAT na wannan shekarar 2021 a Cibiyar Kasuwancin duniya da Ke Birnin Dubai.

Taron Baje Kolin na bana ya janyo masu ruwa da tsaki daga k’asashen duniya dabam dabam ta wajen harkar kirkirar shirye-shirye, dillanci da rarraba hotunan bidiyo.

Taron da za’a shafe kwanaki biyu anayi, daga ranar 26 Zuwa 28 ga watan Oktoba, zai duba tare da tattauna batutuwa da dama domin inganta cigaban harkar dillanci hotunan bidiyo da rarrabawa da kuma watsa shirye shirye da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *