AN GUDANAR DA ZANGA-ZANGAR ADAWA DA SABON SHUGABANCIN HUKUMAR ZA’BE A JAMHURIYYAR DEMOKRADIYAR KONGO

AN GUDANAR DA ZANGA-ZANGAR ADAWA DA SABON SHUGABANCIN HUKUMAR ZA’BE A JAMHURIYYAR DEMOKRADIYAR KONGO

Dubban mutane ne suka fito kan titunan Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo (DRC), domin nuna adawa da matakin da shugaban kasar Felix Tshisekedi ya dauka na nada babban amininsa jagoran hukumar zaben kasar.

Matakin da Tshisekedi ya dauka a watan da ya gabata ya zo ne duk da adawar da ‘yan adawar siyasa da masu fada a ji na Katolika da na Furotesta suka nuna.

Masu suka dai sun ce Denis Kadima, sabon shugaban hukumar Za’be ta CENI ya kasance mai cin hanci da rashawa kuma yana kusa da shugaban kasar.

“Wannan kasarmu ce, kuma babu wanda zai hana mu neman hakkinmu,” in ji wani mai zanga-zanga a Kinshasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *