AN KAMA MASU GARKUWA DA MUTANE 30 A JIHAR IMO
Rahotani daga Jihar Imo na cewa Jami’an tsaro na hadin gwiwa dake sintiri a sansanonin karamar hukumar Orsu da Uli a karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra, sun kama wasu mutane 30 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suka addabi jihar Imo.
Rahoton ya Kara da cewa an ceto wani basaraken gargajiya da aka yi garkuwa da shi a yayin samamen.