AN KAMA WANI MUTUM DA KWAYOYIN TRAMADOL MILYAN 1
An kama wani mutum da ake zargin Mai fataucin miyagun Kwayoyi ne da tramadol miliyan daya, a hanyar Legas zuwan Benin.
Kakakin Hukumar yaki da fataucin miyagun Kwayoyi na Najeriya, Femi Babafemi, ne ya tabbatar da hakan inda yace a ranar 10 ga watan Disamba ne aka kama Onuoha Friday, mai shekaru 43 da haihuwa da kwayoyin.
Babafemi ya kara da cewa jami’an hukumar sun kuma kama wani dan Kasar Ghana da wasu ‘yan Najeriya biyu a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da kuma filin jirgin sama na Akanu Ibiam, dake Enugu, bisa laifin safarar hodar Iblis da methamphetamine mai nauyin kilogiram 9.953.