AN KASHE SOJOJIN WANZAR DA ZAMAN LAFIYA NA MAJALISAR DINKIN DUNIYA A AFRIKA TA TSAKIYA

A kalla sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya uku ne wasu kungiyoyi masu dauke da makamai da ba a san su ba suka kashe a kudu maso gabashin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR).
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Stephane Dujarric, mai magana da yawun Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce wasu ‘yan kungiya ne da ba’a san ko su waye ne ba suka kai ma sojojin kungiyar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da Sojojin Afirka ta Tsakiya hari a lokacin da suke sintiri a Dekoa.
Sanarwar ta kara da cewa “An kashe sojojin kiyaye zaman lafiya uku daga Burundi tare da jikkata wasu biyu.”
Wakilin ya tunatar da masu aikata laifin cewa hare-hare kan sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya na iya zama laifin yaki, tare da yin kira ga hukumomin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da su binciki munanan hare-haren tare da hanzarta hukunta masu laifi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *