AN NADA SANATA ZAYNAB KURE SHUGABAR JAM’IYYAR PDP RESHEN JIHAR NEJA

Jam’iyyar PDP reshen Jihar Neja ta amince da nadin Sanata Zaynab Kure, ta maye gurbin tsohon Gwamna Babangida Aliyu a matsayin shugabar jam’iyyar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Suleiman Aliyu, sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na jihar ya fitar ranar Talata a Birnin Minna.