AN YANKE WA WASU DALIBAI 20 HUKUNCIN KISA BISA LAIFIN KISAN KAI

A yau laraba, ne, Kasar Bangladesh ta yanke wa wasu daliban jami’a 20 hukuncin kisa bisa samun su da laifin kisan wani matashi a shekarar 2019 wanda ya caccaki gwamnati a shafukan sada zumunta.
An tsinci gawar Abrar Fahad mai shekaru 21 da haifuwa a dakin kwanansa na jami’ar, sa’o’i bayan ya rubuta wani sako da ya wallafa a Facebook yana caccakar firaminista Sheikh Hasina kan kulla yarjejeniyar raba ruwa da Kasar Indiya.
Binciken ya gano daliban da aka yanke wa hukuncin ne suka kashe shi ta hanyar yi masa duka da sandunan buga wasan kiriket Saboda adawa da sakon da ya wallafa a shafinsa ta facebook.