AN ZARGI GWAMNONIN KEBBI, JIGAWA DA YOBE DA ‘KULLA MAKARKASHIYAR WARGAZA JAM’IYYAR APC
Wata kungiyar Zamfarawan da ke goyon bayan tsohon gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari Abubakar ta zargi gwamnan Kebbi Abubakar Atiku Bagudu da na Jigawa Mohammed Badaru Abubakar da shugaban rikon jam’iyyar APC na kasa Mai Mala Buni da kulla makarkashiyar watse jam’iyyar APC a Najeriya.
Shugaban kungiyar kuma jigon jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Nabature Nahuche ne yayi wannan zargin a wata ganawa da manema labarai bayan wani taron da kungiyar ta gudanar a garin Gusau.
Nabature Nahuche yace jam’iyyar APC na gab da tarwatsewa muddin ba a taka ma mutanen burki ba a cikin kisisinar da suke kitsawa.
Haka kuma kungiyar ta karyata bayanan dake zagayawa a wasu shafukan yanar gizo masu cewa wai tsohon gwamna AbdulAziz Yari zai fice daga APC zuwa PDP.
Shugaban kungiyar yace tuni aka garzaya kotu kan maganar rushe shugabancin APC na Lawal M. Liman Gwamdon Kaura da maganar zaben shugaban jam’iyyar da bangaren gwamna Matawalle ya gudanar.
Wannan al’amrin dake gudana a jihar Zamfara na nuna cewa da alamun karakaina ko da kwamacalar siyasa a shekarar 2023
www.wtvnigeria.com