Asusun bayar da lamuni na duniya, IMF, ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta cire talafin man fetur da na hasken wutar lntarki

Asusun bayar da lamuni na duniya, IMF), ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta cire talafin man fetur da na hasken wutar lntarki baki daya a farkon shekara mai zuwa.

Wani bincike da asusun ya gudanar a karshen ziyarar da jami’ansa suka kawo Najeriya ya kuma yi kira ga gwamnati ta gudanar da sauye-sauye kan harkokin kudi, da musayar kudin da kasuwanci da kuma mulki “domin sauya tafiyar hawainyar da hanyar ci gaban” kasar take yi..

A wata sanarwa da asusun ya fitar bayan kammala ziyarar, ya ce ya kamata cire tallafin man fetur da na wutar lantarki ya kasance abin da kasar ta fi bai wa fifiko a wani bangare na tsarin harkokin kudi.

Jaridar Daily Trust, wadda ta ambato asusun na yin wadannan kiraye-kiraye, ta ce asusun ya ce ya kamata gwamnati ta bullo da hanyoyin da za su rage kaifin illar da janye tallafin man fetur da na lantarkin za su yi ga rayuwar talaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *