BA ZAMU RUFE JAMI’OIN KARATU BA SABODA BULLAR CUTAR KORON

-Inji Hukumomin Kasar Masar
Gwamnatin Masar ta musanta jita-jitar da ke yaduwa cewa za a dakatar da karatun jami’a sannan a dage jarrabawa saboda bullar kwayar cutar coronavirus, karo na biyu.
Cibiyar yada labarai ta majalisar zartarwar Masar a cikin wata sanarwa a ranar Asabar ta ce ta tuntubi Ma’aikatar Ilimi mai zurfi da Nazarin Kimiyya wanda ya tabbatar da cewa ba za a dakatar da karatu ba.
Wadannan cibiyoyin ilimin za su ci gaba kamar yadda aka saba, in ji ta, tare da gudanar da jarabawa daidai da jadawalin shekarar karatu ta yanzu tare da bin dukkan matakan kariya don dakile barkewar cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *