Bayan kwashe watanni a hannun ‘yan bindigar da suka sace shi, mahaifin Kakakin Majalisar Dokoki ta jihar Zamfara Alhaji Muazu Abubakar Magarya ya rasu a sakamakon bugawar zuciya

Wani dan’uwan marigayin ne mai suna Dahiru Saraki Magarya ya tabbatar da hakan a wata hira da manema labarai da yayi a rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara bayan an samu nasarar kubutar da shi.
Dahiru Magarya yace wani kasurgumin dan ta’adda ne da ake yi ma lakabi da suna Kachalla ya tsegunta ma shi rasuwar dan uwan nasa.
Ita ma matar marigayin mai suna Hauwau Magarya tace ta ji daya daga cikin ‘yan ta’addan dake tsare da su bayan sace su da aka yi na cewa mijinta ya mutu.
A ranar 5 biyar ga watan Ogosta ne na wannan shekarar ta 2021 daruruwan yan bindiga suka kai hari a garin Magarya ta karamar hukumar Zurmi inda suka yi awon gaba da mutane da yawa ciki har da mahaifin Kakakin majalisar dokoki ta jihar Zamfara da wasu ‘yan uwansa.
Duk da matakan da jami’an tsaro ke dauka har yanzu ana samun hare-hare a wasu kauyukan jihar, amma jami’an tsaro sun ce ana samun gagarumar nasara.
Kuma ko a cikin watan Satumba da ya gabata wasu ‘yan bindiga sun kai mummunan hari a garin inda suka kone wasu gidaje da dama.

GUDUMMAWA:

Tabbatar da tsabtataccen aikin jarida, abu ne da ke da muhimmin amfani wajen wanzuwar zaman lafiya, ilimantar da al’umma kan lamuran yau da kullum, da kuma kauracewa duk wani abinda zai jawo rudani ko tashin hankali. A dalilin haka ne muke bukatar gudummawarku domin dorewar wannan kokarin. Domin bada gudammawa, ga bayanan asusun banki:

Jaiz Bank Account lamba:

0001741269

Wonderland Television ltd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *