CHADI ZA TA TURA ‘KARIN SOJOJI DUBU 1,000 KASAR MALI
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Mali ta bayyana cewa, kasar Chadi na shirin tura karin sojoji 1,000 zuwa kasar Mali domin karfafa dakarunta da ke yaki da masu tada kayar baya, a daidai lokacin da Faransa ke rage yawan sojojinta a yankin Sahel na Afirka.
Kawo yanzu, Sojojin Chadi kusan 1,400 ne ke taya dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya 13,000 dake arewaci da tsakiyar kasar Mali, inda rikicin ta’addanci ya yi kamari.