El-RUFAI YA BUKACI A AYYANA ‘YAN BINDIGA, ‘YAN TA’ADDA
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya roki Gwamnatin Tarayya da ta ayyana ‘yan bindiga da su ka addabi yankin Arewa maso Yammacin kasar, a matsayin ‘yan ta’adda.
Hakan Inji shi zai karfafa wa sojoji karfin gwuiwan kai farmaki da kashe ‘yan bindigan ba tare da fargaban wani dokar kasa da kasa ba.
El-rufai, ya bayyana hakan ne, ranar Laraba, yayin da ya ke karbar rahoton tsaro na kwata na uku daga Kwamishinan Tsaro na cikin gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan.