FARAREN HULA 11 SUN MUTU A WANI ARANGAMA TSAKANIN SOJOJI DA ‘YAN TAWAYE A JAMHURIYYAR AFIRKA TA TSAKIYA

  • FARAREN HULA 11 SUN MUTU A WANI ARANGAMA TSAKANIN SOJOJI DA ‘YAN TAWAYE A JAMHURIYYAR AFIRKA TA TSAKIYA

Fararen hula 11 ne aka kashe a yankin arewa maso yammacin jamhuriyar Afrika ta tsakiya sakamakon gwabza fada tsakanin ‘yan tawaye da sojoji, duk da tsagaita bude wuta da aka yi a kasar, kamar yadda karamar hukumar ta sanar a ranar Talata.

‘Yan tawayen “sun kutsa kai ne cikin kasuwar mako-mako da misalin karfe 10 na safiyar Lahadi, kusa da Mann, wani gari mai tazarar kilomita 600 (mil 370) arewa maso yammacin Bangui”, kamar yadda Dieudonne Yougaina, shugaban karamar hukumar Ouham-Pende, ya sanar.

“Dakarun Afirka ta tsakiya sun shiga tsakani… kuma musayar wuta ne ya yi sanadin mutuwar fararen hula 11, maza tara da mata biyu, yayinda da wasu takwas suka jikkata,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *