FIRAMINISTAN KASAR SUDAN ABDALLA HAMDOK YAYI MURABUS

Rahotani daga birnin Khartoum na cewa firaministan Sudan, Abdalla Hamdok ya yi Murabus makonni shida bayan mayar da shi kan mukaminsa a wani bangare na yarjejeniya da sojojin da suka hambarar da gwamnati tun a watan Oktoba.
A wani jawabi da aka watsa ta talabijin, Hamdok ya ce “Na yanke shawarar sauke wannan nauyi da kuma sanar da yin murabus a matsayin Firayim Minista”.