FIRAYIM MINISTAN HABASHA YA JAGORANCI DAKARUN SOJA ZUWA FAGEN DAGA

FIRAYIM MINISTAN HABASHA YA JAGORANCI DAKARUN SOJA ZUWA FAGEN DAGA
Rahotani daga Habasha na cewa Firayim Ministan ‘kasar, Abiy Ahmed, ya je fagen daga domin jagorantar dakarunsa a yakin da suke yi da ‘yan tawayen yankin arewacin Tigray, kamar yadda kafafen yada labarai masu alaka da gwamnati suka ruwaito.
Mataimakin Firayim ministan kasar, Demeke Mekonnen Hassen, ne zai jagoranci harkokin gwamnati na yau da kullun, kafin dawowar Firaministan Abiy, in ji kafar yada labarai ta Fana a ranar Laraba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *