GHANA TA HARAMTAWA DUK WANDA BAI YI ALLURAR RIGAKAFIN KORONA BA SHIGA KASAR
Ghana ta ba da Sanarwar haramtawa duk wani baligi da ba a yi masa allurar rigakafin cutar Korona ba shiga Kasar daga ranar Litinin mai zuwa.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Ghana, Patrick Kuma-Aboagye, Wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa yace tilas ne ayi wa duk baligin da ya sauka Ghana allurar idan bai yi a baya ba.
Sanarwar ta ce an dau Matakin ne don gudun yaduwar cutar daga matafiya da za su zo hutun karshen Shekara daga Kasashe daban-daban.
www.wtvnigeria.com