GOBARA TA KASHE FURSUNONI 38 A GIDAN YARI

Akalla fursunoni 38 ne suka mutu yayin da 69 suka samu munanan raunuka bayan da wata gobara ta tashi a babban gidan yari da ke Gitega babban birnin kasar Burundi a ranar Talata, kamar yadda mataimakin shugaban kasar, Prosper Bazombanza ya shaidawa manema labaru.
Sai dai bai bayyana ko mene ne ya haddasa gobarar ba, amma wasu mazauna yankin sun ce gobarar ta tashi ne kafin wayewar gari, kuma yawancin waɗanda suka mutu tsofaffin fursunoni ne.