GUGUWA TA KASHE AKALLA MUTANE 70 A AMURKAF
Fiye da mutane 70 ake fargabar sun mutu, bayan wata mummunar guguwa da ta afku a jihar Kentucky da wasu jihohin Amurka, da yammacin Juma’a da kuma safiyar Asabar.
Gwamnan Jihar Kentucky, Andy Beshear ne ya shaidawa wani taron manema labarai hakan, da sanyin safiyar Asabar, inda ya bayyana guguwar a matsayin mafi muni da
ba’a taɓa fuskanta a Jihar ba, yana mai cewa “barnar bata misaltuwa, wanda a dalilin haka na ayyana dokar ta-baci”.