GWAMNA TAMBUWAL YA NEMI SHUGABA BUHARI YA AYYANA DOKAR TA-BACI A DUK SANSANONIN YAN TA’ADDA

GWAMNA TAMBUWAL YA NEMI SHUGABA BUHARI YA AYYANA DOKAR TA-BACI A DUK SANSANONIN YAN TA’ADDA

 

FB_IMG_1639460375479

 

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya kafa dokar ta-baci a duk yankunan da masu aikata muggan laifuka da ‘yan ta’adda Ke cin Karensu ba babbaka.

Yin hakan a cewar Gwamna Tambuwal wanda ya gana da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa da yammacin litinin, zai baiwa rundunar soji damar gudanar da ayyukansu ba tare da cikas ba a dukkan yankunan.

“Muddin hakan ya tabbata, ya ​​kamata a yi su lokaci guda a jihohin da ‘yan ta’adda ke da sansani, irin su, Sokoto, Zamfara, Katsina, Kaduna, Niger da Kebbi; da kuma sauran wurare, inda masu aikata manyan laifuka ke da maboya,” in ji sanarwar da mai ba Gwamnan Shawara na musamman kan harkokin yada labaru, Muhammad Bello, ya fitar
www.wtvnigeria.com

GUDUMMAWA:

Tabbatar da tsabtataccen aikin jarida, abu ne da ke da muhimmin amfani wajen wanzuwar zaman lafiya, ilimantar da al’umma kan lamuran yau da kullum, da kuma kauracewa duk wani abinda zai jawo rudani ko tashin hankali. A dalilin haka ne muke bukatar gudummawarku domin dorewar wannan kokarin. Domin bada gudammawa, ga bayanan asusun banki:

Jaiz Bank Account lamba:

0001741269

Wonderland Television ltd

Leave a Reply

Your email address will not be published.