GWAMNATIN NAJERIYA TA KARA ALBASHIN ‘YAN SANDA DA KASHI 20Hey
Majalisar Zartarwa ta Tarayya, FEC, ta amince da karin kashi 20 cikin 100 na albashi ga rundunar ‘yan sanda daga watan Janairun 2022.
Ministan harkokin ‘yan sanda, Maigari Dingyadi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa a karshen taron tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.
Dingyadi ya ce karin albashin yana daya daga cikin hanyoyin inganta alaka tsakanin rundunar da al’ummar Najeriya.
www.wtvnigeria.com