HABASHA TA RUFE MAKARANTU DOMIN BAI WA DALIBAI DAMAR GIRBE ABINCI GA JARUMAN DA KE BAKIN DAGA
Hukumomin kasar Habasha sun rufe dukkan makarantun sakandare na mako biyu domin dalibai su girbe amfanin gona ga wadanda ke fagen daga na yakin basasa, in ji kafafen yada labarai masu alaka da gwamnati.
Kawo yanzu, fiye da dalibai miliyan 2 ne ba sa zuwa makaranta saboda yakin da aka fara a yankin arewacin kasar a shekarar da ta gabata, in ji gwamnati.
Yayin da fadan ke kara tsanani, sojojin gwamnati sun ce sun karbe wasu garuruwa daga hannun ‘yan tawayen Tigray.