HUKUMAR EFCC TA CAFKE WASU ‘YAN DAMFARA A SOKOTO

HUKUMAR EFCC TA CAFKE WASU ‘YAN DAMFARA A SOKOTO

Hukumar Yaki da Laifukkan da Suka Shafi Kudi da yi ma Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), reshen jihar Sakkwato, ta gabatar da wasu mutane biyu da ake zargi da damfarar samar ma mutane aiki.

Da yake gabatar da wa’yanda ake zargi ga manema labarai, Shugaban ofishin Hukumar, reshen Jihar Sokoto, Bawa Usman Kaltingo yace an kama sune bayan sun yi ma wasu mutane 26 alkawarin bugi na samar masu aiki a Hukumar Shige da Fice ta Kasa (Nigeria Immigration Service).

Usman Kaltingo yace mutanen da ake zargi da yin damfarar suna da wani abokin hadin baki ne a Hukumar Fice da Shigen wanda ya taimaka wurin aikata zambar.

“Ma’aikacin Shige da Ficen da ake zargi ya taimaka ne wurin tsara shirin horas da ma’aikatan na bugi tare da taimakon wani dan banga wanda ya taka rawar mai horaswa a wani dandalin karbar horo na bugi”, Inji Usman Kaltingo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *