Hukumar EFCC ta kama Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ogun, Honorabul Olakunle Oluomo a filin jirgi na Muhammad Murtala dake birnin Legas.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama Kakakin Majalisar ne da safiyar yau Alhamis.
Hukumar EFCC na zargin Olakunle Oluomo da aikata laifuka da suka shafi yin sama da fadi da dukiyar gwamnati.
Sai dai ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu bayanai daga hukumar EFCC game da kame Kakakin Majalisar na Jihar Ogun.
Amma wasu majiyoyi daga hukumar EFCC sun ce hukumar ta sha gayyatar kakakin majalisar ta jihar Ogun don amsa wasu tambayoyi, sai dai yayi biris da goron gayyatar.