HUKUMAR NDLEA TA CAFKE WANI MATASHI DA HODAR IBLIS NA NAIRA BILYAN 2.7

ndl
HUKUMAR NDLEA TA CAFKE WANI MATASHI DA HODAR IBLIS NA NAIRA BILYAN 2.7
Jami’an Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, sun kama wani matashi Maduabuchi Chinedu, mai shekaru 32 da haihuwa, a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja, dauke da hodar iblis mai nauyin kilogiram 9.30 wanda kudinsu ya kai sama da Naira biliyan 2.7.
Wanda ake zargin, haifaffen ‘dan kauyen Okigwe ne dake karamar hukumar Okigwe ta jihar Imo, Kuma mazaunin ‘kasar Laberiya, inda yake aikin hakar ma’adinai, kamar yadda ya bayyana wa Jami’an NDLEA.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *