HUKUMOMIN ‘KASAR LIBYA SUN TSARE BA’KIN HAURE SAMA DA DUBU 5,000 A WANI KAME DA SUKA YI RANAR JUMA’A

HUKUMOMIN ‘KASAR LIBYA SUN TSARE BA’KIN HAURE SAMA DA DUBU 5,000 A WANI KAME DA SUKA YI RANAR JUMA’A

Adadin bakin haure da ‘yan gudun hijirar da ake tsare da su, sakamakon wani kame da Hukumomin ‘kasar Libya su ka gudanar a yammacin ‘kasar, ya zarce Mutane 5,000, ciki har da daruruwan mata da kananan yara, a cewar alkaluman Majalisar Dinkin Duniya.

Daga cikin wadanda aka tsare, 215 yara ne, sama da 540 Kuma mata ne, yayinda akalla 30 daga cikinsu suna da juna biyu, kamar yadda Hukumar Kula da Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) ta shaida wa kamfanin dillacin labarai na Associated Press, ranar Litinin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *