JAMI’AN TSARO A JIHAR IMO SUN MUSANTA YIN MUSAYYAR WUTA TSAKANINSU

JAMI’AN TSARO A JIHAR IMO SUN MUSANTA YIN MUSAYYAR WUTA TSAKANINSU
Wata sanarwar hadin gwiwa tsakanin rundunar sojojin Najeriya da ta ‘yan sanda a jihar Imo ta karyata labaran dake zagaya wa a kafofin yanar gizo wai cewa sun yi musayar wuta a tsakaninsu.
Sanarwar mai dauke da sa hannun Captain Joseph Baba Akubo da CSP Michael Abattam tace labarin musayar wutar wani kinibibi ne da wasu miyagun mutane suka kitsa don nuna cewa akwai rashin jituwa a tsakanin jami’an tsaro a jihar.
Sanarwar ta kara da cewa jami’an tsaro a jihar za su cigaba da aiki tare ba tare da bambanci ba, don haka suna neman hadin kan dukkan al’ummar jihar saboda samun nasara.