JAMI’AN TSARO SUN HARBE MASU ZANGA-ZANGA 5 A ‘KHARTOUM, ‘KASAR SUDAN

JAMI’AN TSARO SUN HARBE MASU ZANGA-ZANGA 5 A ‘KHARTOUM, ‘KASAR SUDAN

Masu zanga-zanga biyar ne aka kashe a ranar Asabar yayin da dimbin jama’a suka fito Zanga-zanga a babban birnin kasar Sudan Khartoum da wasu biranen kasar domin nuna adawa da kwace ikon da sojoji suka yi, in ji shaidu da likitoci.

Zanga-zangar dai ta zo ne kwanaki biyu bayan da babban hafsan sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan ya sanar da sabuwar majalisar mulkin da ta kebe kawancen farar hula da sojoji ke raba madafun iko dasu tun shekar 2019.

Rahotani na cewa Jami’an tsaron sun yi yunkurin tarwatsa masú Zanga-zangar tun da sanyi Safiya ta hanyar korar su da harba borkonon tsuhuwa.

“Sun harba hayaki mai sa hawaye tare da korar masu zanga-zangar kan tituna don hana su isa wurin taron tsakiyar kasar”, in ji shaidu.

GUDUMMAWA:

Tabbatar da tsabtataccen aikin jarida, abu ne da ke da muhimmin amfani wajen wanzuwar zaman lafiya, ilimantar da al’umma kan lamuran yau da kullum, da kuma kauracewa duk wani abinda zai jawo rudani ko tashin hankali. A dalilin haka ne muke bukatar gudummawarku domin dorewar wannan kokarin. Domin bada gudammawa, ga bayanan asusun banki:

Jaiz Bank Account lamba:

0001741269

Wonderland Television ltd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *