JAMI’AN TSARO SUN KASHE ‘YAN BIDIGA 32, YAYIN DA ‘YAN SANDA 5 SU KA RASA RANSU

JAMI’AN TSARO SUN KASHE ‘YAN BIDIGA 32, YAYIN DA ‘YAN SANDA 5 SU KA RASA RANSU

Jami’an tsaron hadin gwiwa na Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 32 da ke tserewa daga Zamfara, a jihar Neja, ranar Lahadi da ta gabata.

Hakan ya faru ne lokacin da ‘yan bindigan suka kai hari kan wani ofishin ‘yan sanda da ke Bangu Gari, a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja, suka harbe’ yan sanda biyar, yayin musayar wuta.

Wata majiyar tsaro ta shaida wa PRNigeria cewa ’’Yan bindigan sun zo da yawansu dauke da manyan makamai ciki har da masu harba makamin roka, bayan sun tsere daga sansanin su da ke Danjibga da Munhaye a karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara”.

“Bayan samun sakon aukuwar lamarin, aka tura tawagar jami’an tsaro na hadin gwiwa, inda su ka yi nasarar yi wa ‘yan ta’addan da ke tserewa ta hanyar Tegina kwanton bauna, suka kashe akalla 32 daga cikinsu, da suka hada da wasu shugabanninsu, kamar su Karki Buzu, da Yalo Nagoshi yayin da Ali Kawaji ya samu munanan raunuka na bindiga,” in ji majiyar.

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *