JAMI’AN TSARON FIRAMINISTAN KASAR SOMALIYA SUN TARU A WAJEN FADAR SHUGABAN KASA

Daruruwan sojoji masu biyayya ga firaministan Somaliya Mohammed Hussein Roble sun yi sansani a ranar Talata a kusa da gidan abokin hamayyarsa na siyasa Mohamed Abdullahi Mohamed, kwana guda bayan da shugaban kasar ya yi yunkurin dakatar shi.
Roble ya kira shirin shugaban kasar na dakatar da shi a matsayin yunkurin juyin mulki.
Wata sanarwar da Amurka ta fitar a Somaliya inda ke yaki da masu kaifin kishin Islama, ta yi kira ga dukkan bangarorin da su kaucewa tabarbarewar lamarin amma kuma da alama tana goyon bayan firaministan.
Rahotani na nuna jami’an tsaron ba su dauki wani mataki ba har zuwa yammacin ranar Talata, sai dai sansani da suka yi a wajen fadar shugaban kasa ya haifar da fargabar barkewar rikici tsakanin dakarun da ke biyayya ga mutanen biyu.