JAMI’AN TSARON ‘KASAR SUDAN SUN CAFKE SHUGABAN OFISHIN GIDAN TALABIJIN ALJAZEERA A BIRNIN KHARTOUM

JAMI’AN TSARON ‘KASAR SUDAN SUN CAFKE SHUGABAN OFISHIN GIDAN TALABIJIN ALJAZEERA A BIRNIN KHARTOUM
Jami’an tsaron kasar Sudan sun kai samame gidan shugaban ofishin gidan talabijin na Aljazeera a birnin Khartoum, da daren lahadi, tare da kama shi, kwana guda bayan zanga-zangar nuna adawa da mulkin soja da dubban ‘Yan Kasar suka gudanar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar “Al Jazeera ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan abin da sojoji suka aikata tare da yin kira ga hukumomi da su gaggauta sakin El Kabbashi tare da barin ‘yan jaridar su gudanar da ayyukansu ba tare da tsangoma ba.”
Sai dai kawo yanzu Hukumomin ‘kasar Sudan ba su bayar da wani dalilin tsare El Kabbashi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *