JIHOHIN BENUE, ONDO, EKITI, EBONYI DA TARABA SUN SHIGA SAHUN JIHOHI 22 DA SUKA NUNA SHA’AWAR FARA SHIRIN NAU’IN KIWO TA GWAMNATIN TARAYYA

JIHOHIN BENUE, ONDO, EKITI, EBONYI DA TARABA SUN SHIGA SAHUN JIHOHI 22 DA SUKA NUNA SHA’AWAR FARA SHIRIN NAU’IN KIWO TA GWAMNATIN TARAYYA

Akalla jihohi 22 ne suka rubutawa gwamnatin tarayya wasika domin nuna sha’awarsu ta shiga shirin kawo sauyi na kiwo na kasa ta NLTP, da wasu ke ‘kira Ruga.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin noma, Andrew Kwasari, wanda kuma shi ne mai kula da sabuwar Shirin kiwon dabbobi ta NLTP, ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce jihohin sun hada da, Kaduna, Benue, Taraba, Adamawa, Plateau, Zamfara, Kano, Ondo, Katsina, Bauchi, Yobe, Borno, Gombe, Nasarawa, Niger, Sokoto, Ekiti, Kogi. Ebonyi da Kwara.

Andrew Kwasari ya bayyana cewa sati mai zuwa Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan jihohin da suka nuna sha’awarsu na shiga Shirin kudaden da aka ware don aiwatar da nau’in kiwon dabbobin a fadin Kasar.

Ya kara da Cewa gwamnatin tarayya ta Fito da Shirin ne don magance rikice-rikicen da aka da’de ana fama da shi tsakanin manoma da makiyaya.

“Gwamnatin tarayya a shekarar 2018 ta fito da nau’o’in kiwo iri-iri da suka hada da Ruga da NLTP domin samarwa makiyaya wadanda galibi Fulani ne wuraren kiwo na musamman”, Inji Andrew

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *