JIRGIN SAMA MAI SAUKAR UNGULU DAUKE DA SHUGABAN HAFSAN TSARON KASAR INDIA DA MATARSA YA YI HADARI

JIRGIN SAMA MAI SAUKAR UNGULU DAUKE DA SHUGABAN HAFSAN TSARON KASAR INDIA DA MATARSA YA YI HADARI
May be an image of 5 people, people standing and outdoors
Wani jirgin sama mai saukar ungulu dauke da babban hafsan sojan Indiya, Bipin Rawat, da Mai dakinsa ya fado kusa da garin Ooty a Tamil Nadu, ranar Laraba.
Majiyoyi sun ce an kai akalla mutane uku da suka jikkata sakamakon hadarin zuwa wani asibiti da ke kusa, yayinda ake dakon cikakken bayanai na wadanda suka jikkata da kuma irin hasarar da aka samu.
Da take tabbatar da faruwar lamarin a shafin Twitter, rundunar sojin saman Indiya ta ce an bayar da umarnin gudanar da bincike don gano musabbabin hatsarin jirgin.

GUDUMMAWA:

Tabbatar da tsabtataccen aikin jarida, abu ne da ke da muhimmin amfani wajen wanzuwar zaman lafiya, ilimantar da al’umma kan lamuran yau da kullum, da kuma kauracewa duk wani abinda zai jawo rudani ko tashin hankali. A dalilin haka ne muke bukatar gudummawarku domin dorewar wannan kokarin. Domin bada gudammawa, ga bayanan asusun banki:

Jaiz Bank Account lamba:

0001741269

Wonderland Television ltd

Leave a Reply

Your email address will not be published.