KARUWANCI DA SHAYE-SHAYEN MUGGAN KWAYOYI NA CIKIN DALILAN RUFE SANSANONIN YAN GUDUN HIJIRA
-Inji Gwamna Zulum

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana dalilan da suka sa aka rufe sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Maiduguri, inda ya ce sansanonin sun fara zama dabar da ake tafka munanan ayyuka da suka hada da karuwanci, shaye-shayen miyagun kwayoyi da ayyukan ‘yan daba, wasu lokuta.
Farfesa Zulum ya lura cewa babu wani shugaban kwarai da zai bar mutane su yi rayuwa marar mutunci a karkashin sa.
Hakan na kunshe ne a cikin sakon sabuwar shekara da aka aika wa ‘yan jihar Borno ranar Asabar a Maiduguri, babban birnin jihar.
Gwamnan ya kara da cewa dalilin bude sansanonin ‘yan gudun hijira wani mataki ne na wucin gadi na samar da tsaro musamman a lokacin da ake fama da tashe tashen hankula, ba wai ana nufin sansanonin su ci gaba da wanzuwa har abada ba.