BURTANIYA TA TURA SOJOJI GIDAJEN MAI DON SHAWO KAN MATSALAR RASHIN MAI A FADIN KASAR.
Kasar Burtaniya ta Bada Sanarwar aika Jami’an soji 200 gidajen mai don shawo kan Matsalar rashin Mai da aka kwashe mako guda ana fama da shi a fadin Kasar.
Kawo yanzu, kusan Kashi 80 na gidajen mai da Ke fadin Kasar na rufe Saboda karancin matuka manyan motoci, Lamarin ya jawo rudani, da suka hada da dambe tsakanin masú ababen hawa da yawo da mai a kwalaben ruwan sha.
Gwamnatin Burtaniyan ta ce daga ranar Litininin Mai Zuwa, Jami’an Sojin za su fara aiki a gidajen man. “Yanzu haka, muna horar da Jami’an 200,Wanda 100 daga cikinsu direbobin manyan motoci ne”,