JIRAGE MASU SAUKAR ANGULU DA ‘KASAR MALI TA SAYA DAGA RASHA SUN ISA BIRNIN BAMAKO
Wani jirgin daukar kaya daga Kasar Rasha ya sauka a Babban filin Jiragen sama na Bamako dauke da helikwafta guda hudu, da makamai da albarusai.
Ministan tsaro na wucin gadi na Kasar Mali, Sadio Camara, Wanda ya tabbatar da hakan ya ce Mali ta sayi jiragen ne a cikin wata kwangilar da aka amince da ita a watan Disambar shekarar 2020 don tallafa wa dakarunta a yaki da ta’addanci da suke yi- tare da hadin gwuiwan sojojin Faransa, na Turai da na Majalisar Dinkin Duniya.
Ministan ya kara da cewa makamai da albarusai da aka sauken na daga cikin kyaututtuka daga Kasar ta Rasha.