KIMANIN MUTANE BILYAN 2.9 BA SU TA’BA AMFANI DA YANAR GIZO BA – Rahoton Majalisar Dinkin Duniya
Kimanin mutane biliyan 2.9 ne a duniya da har yanzu ba su taba amfani da yanar gizo ba kuma kashi 96 daga cikinsu na rayuwa ne a kasashe masu tasowa, kamar yadda wani sabon rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya gano.
A cewar Kungiyar Sadarwa ta Duniya (ITU), kiyasin adadin mutanen da suka shiga kan layin yanar gizo a cikin shekarar 2021 a zahiri sun haura, zuwa biliyan 4.9