Ko Kun san sabon shugaban jamiyyar PDP ta kasa ?

Masú Ruwa da tsaki a Jam’iyyar PDP, daga arewacin Najeriya, sun amince da tsohon shugaban majalisar dattijai, Sanata Iyorchia Ayu, a matsayin dan takarar su na shugaban jam’iyyar na kasa a babban taron kasa da za’a gudanar ranar 30 ga watan Oktoba mai zuwa.

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar ranar Alhamis a masaukin Gwamnan Jihar Bauchi, da ke Asokoro, a Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *