KOTU TA AMINCE WA SEIF GADDAFI TSAYAWA TAKARAR SHUGABAN KASAR LIBYA
Wata kotu a kudancin Libya a ranar Alhamis ta amince Seif al-Islam Gaddafi, dan marigayi Moamer Gaddafi, ya tsaya takara a zaben shugaban kasa da za a gudanar a wata mai zuwa, kamar yadda kafafen yada labarai na Libya suka ruwaito.
Hakan ya biyo bayan karar da Seif ya shigar da safiyar Alhamis, a kotun da ke Sebha kan kin amincewar da hukumar zabe ta yi na bukatarsa na tsayawa zabe a watan jiya.
A watan da ta gabata ne wani mai shigar da kara na soji a birnin Tripoli ya bukaci hukumar da ta dakatar da Gaddafi daga tsayawa takara saboda a shekarar 2015 an yanke masa hukunci kan laifukan yaki
www.wtvnigeria.com