KUNGIYAR ECOWAS ZA TA GUDANAR DA TARON KOLI RANAR LAHADI A ABUJA
A ranar Lahadi 12 ga watan Disamba ne shugabannin kungiyar ECOWAS za su gudanar da wani taro na yau da kullun a Abuja, babban birnin Najeriya.
Shugabannin za su tattauna batutuwa da dama da suka hada da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi a yankin, da aiwatar da kudin bai-daya, da kuma rikicin siyasar Mali da Guinea, wadanda suka fuskanci juyin mulki a ‘yan watannin nan.
Taron zai kuma Tattauna Mafita kan kasar Mali wadda shugabanninta suka kasa cimma matsayar gudanar da zabe a ranar 27 ga watan Fabrairun 2022, sabanin alkawarin da suka yi a baya.
www.wtvnigeria.com