KWAMINITIN RIKO NA GWAMNA BUNI NE SILAN SABON RIKICIN JAM’IYYAR APC A JIHAR ZAMFARA – Cewar Sanata Marafa

KWAMINITIN RIKO NA GWAMNA BUNI NE SILAN SABON RIKICIN JAM’IYYAR APC A JIHAR ZAMFARA
– Cewar Sanata Marafa

Wani jigo a jam’iyyar APC mai mulki a Zamfara, Sanata Kabir Marafa ya zargi shugabannin jam’iyyar na kasa da alhakin sabanin da a ka samu wajen gudanar da taron gundumomi a jihar ranar Asabar.
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja ranar Lahadi, Marafa wanda bangarensa ya gudanar da wani taron kama-da-wane a daukacin gundumomi 147 na kananan hukumomi 14, ya ce ya kamata kwamitin riko na kasa ya dauki alhakin sabon rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar a jihar.
A cikin watan Yuni da ya gabata ne jam’iyyar APC ta dakatar da taron zaben shugabannin majalisar a dukkan matakai na jihar Zamfara bayan da Gwamna Bello Matawalle ya sauya sheka, daga PDP Zuwa APC
#wtvnigeria

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *