KWAMISHINAN ‘YAN SANDAN JIHAR ZAMFARA YA KAI ZIYARAR GANI DA IDO WURARE DA AKA GIRKE JAMI’AN YANSANDA

KWAMISHINAN ‘YAN SANDAN JIHAR ZAMFARA YA KAI ZIYARAR GANI DA IDO WURARE DA AKA GIRKE JAMI’AN YANSANDA

kokarin da yake yi na magance kalubalen tsaro akan hanyar Kauran Namoda zuwa Shinkafi, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara CP Ayuba El kana ya kai ziyara zuwa wurare ukku da aka girke dakarun tsaro wadanda suka hada da Dan Bita! Dogon Karfe, da Hawan Bakwai da kuma kwanar Jaloop dake karamar hukumar Shinkafi.

Wannan na kunshe ne a cikin wata takardar manema labarai mai dauke da sa hannun Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar SP Mohammed Shehu.

Takardar tace dalilin ziyarar shine don Kwamishinan ya gane ma idonsa irin shirin na dakarun samar da tsaro da aka yi akan hanyar da niyyar karfafa masu don samar da cikakken tsaro

CP El kana ya tabbatar ma dakarun cewa babban sifetan ‘yan sanda IGP Usman Alkali Baba yana sane da sadaukar da kan da suke yi a yakin da ake yi da ayukkan ta’addanci.

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *